News
An Saka Dokar Hana Fita A Jihar Gombe.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta sanya dokar hana fita daga Karfe 12 na tsakar dare zuwa karfe 6 na safe, a wani mataki data dauka biyo bayan kisan gillar da aka yi wa wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Albani
A ranar Laraba ne aka halaka Sheikh Ibrahim Musa Albani a gidansa dake Gombe.
Akpabio Ya Yi Suɓul-da-baka Kan ‘Kuɗaɗen More Hutun’ Sanatoci
Majiyar ‘yan uwansa ta ce wasu mutane hudu dauke da adduna rufe fuskokinsu sun farwa malamin addinin musuluncin tare da halaka shi har lahira a gidansa da ke unguwar Tabra a jihar Gombe da misalin karfe 3 na dare.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Oqua Etim ne ya bayar da umarnin saka dokar hana fitar kamar yadda yake cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar jihar ASP Mahid Abubakar ya fitar.
Duk da cewar Dokar hana fitar zata hana mutane samun sukuni kamar yadda rundunar ta baiyana, Sai dai ta ce dokar na da nufin kiyaye lafiyar jama’a, da dakile yawaitar ayyukan ta’addanci, da kuma tabbatar da doka da oda a fadin jihar.