News
Likitoci Sun Janye Yajin Aiki Da Suka Tsunduma
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa NARD ta janye yajin aikin da ta tsunduma na sai baba-ta-gani a fadin kasar nan makonni biyu da suka gabata.
Wannan shawarar ta zo ne bayantattaunawa tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayya inda shugabannin kungiyar suka umurci dukkan mambobinta da su koma bakin aikin a yau Asabar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Emeka Orji ya fitar inda ya nuna cewa za su sa ido sosai kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma da gwamnati.
A cewar shugaban kungiyar ta NARD, likitocin na bayar da shawarwari ne kan muhimman abubuwa guda takwas da suka hada da daukar karin ma’aikata domin cike gurbin likitocin da suka yi hijira ko kuma suka rasu.
Yan kungiyar mu suna shan wahala. ‘Yan Najeriya ma suna shan wahala. Lokacin da ba ku da adadin likitoci a asibiti, babu yadda za a yi ba zai shafi tsarinkiwon lafiya ba. Kuma babu wanda ya fito ya gaya mana cewa abin da muke fada ba gaskiya ba ne,” in ji shi.
“Gwamnati da kanta ta kafa kwamitin ministocin da ya fito da tsari tun watan Fabrairun wannan shekara, me ya sa ba a aiwatar da wannan tsarin ba?”
Tun da farko dai likitocin da suka shiga yajin aikin sun bayar da wa’adin sa’o’i 72 domin a biya musu bukatunsu kafin su kawo karshen yajin aikin.