News
Rundunar Sojojin Nijeriya sun soki masu kira kan su yi katsalandan a dimokuradiyyar kasar nan

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN.
Hedikwatar tsaron kasa ta yi watsi da masu kira kan sojojinta da su yi katsalandan a tsarin dimokradiyyar kasar nan.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Asabar, ta ce sojojin kasar sun nuna rashin jin dadinsu kan wani labari da ake watsawa a yanar gizo kan cewa akwai wasu matsaloli game da batun jin dadi da walwalwa na sojojin kasar.
Sanarwar ta ce shugaban sojin kasar Janar CG Musa ya kara jaddada biyayyarsa ga Shugaba Tinubu inda ya ce ba zai kauce wa aikinsa da kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya tsara ba.
“Kiraye-kirayen da ake yi kan sojoji da su yi katsalandan a dimokradiyya rashin kishin kasa ne, da mugunta da kuma yunkurin kawar da hankalin sojojin Nijeriya daga gudanar da ayyukansu da kundin tsarin mulki ya tsara,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
“Ganin cewa rundunar sojin Nijeriya tana mayar da hankali wurin kyautata wa dakarunta, ba mu kaunar duk wani yunkuri na wani ko wata kungiya da za ta harzuka Sojojin Nijeriya masu bin doka domin su tunkari sauyin gwamnati wanda kundin tsarin mulkin kasar bai amince da shi ba.
“Muna so mu bayyana cewa ba shakka sojoji suna farin ciki kuma sun fi dacewa a karkashin mulkin dimokradiyya kuma ba za su shiga duk wani aiki na zagon kasa ga dimokradiyyar da aka samu a kasarmu ba,” in ji sanarwar.