News
Hukumar PCCAC Ta Samu Nasarar Kama Wasu Mutum Biyu Da Damfarar Aminu Dantata Da A.T. Gwarzo.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta samu nasarar kama wasu mutane biyu Bukar Galadima da Sulaiman Ahmed sakamakon damfarar shahararren mai kuɗin nan Alhaji Aminu Dantata da kuma tsohon minista,A.T. Gwarzo.
Haka kuma Hukumar ta yi nasarar kwato kuɗi Naira Miliyan 5 a hannun wadanda aka kama.
Manchester United Ta Kori Mai Horas Da Ƴan Wasanta Erik Ten Hag
Da yake zantawa da jaridar SOLACEBASE jim kadan bayan kammala zaman kotun, lauyan masu shigar da kara Zahraddeen Hamisu Kofarmata ya ce masu laifin Bukar Galadima da Sulyman Ahmed sun hada baki ne inda suka yi nasarar aiwatar da damfara.
Rahotanni sun bayyana cewa Bukar Galadima ya yi karyar cewa shi tsohon ministan babban birnin tarayya, ne inda ya ke nemarwa Mohammed Abba Gana wanda ba shi da lafiya taimakon kudin jinya na miliyan biyar a hannun Ɗantata.
Nan take Dantata ya bukace da ya aiko da lambar asusun bankin sa inda suka tura na matar sa mai suna Sadiyya Abba inda ya aika musu da Naira miliyan biyar.Haka Shi ma kuma Tsohon Minista A.T Gwarzo da irin wannan bukata su ka je masa inda suka nemi Naira Miliyan daya a hannun sa.
Wanda ya karbi kudin ya aikawa mutumin da ya taya shi damfara kuɗi N500,000 inda shi kuma ya soke N5m.
Baiyi wata wata ba Aminu Dantata ya kira tsohon ministan domin jin halin da yake ciki game da jinyar inda a nan ne ya gane an zambace shi.
Nan take Aminu Dantata ya kai rahoto ga hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano inda nan take ta fara gudanar da bincike.
A yanzu haka dai Kotun da ke karkashin jagorancin Umma Sani Kurawa ta yanke musu hukuncin daurin watanni 6 a gidan yari ko kuma su biya tarar Naira 30,000 kowannensu, da daurin watanni 3.
Hakazalika, an kuma umarce su da su biya diyyar N 5, 000, 000 ko kuma su yi zaman kaso na shekaru 2 a gidan yari.
