Labarai
Kungiyar Awareness For Human Right And Charity Foundation Ta Bayar Da Kyautar Jini Leda 150 A Kano

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kungiyar kare hakkin Dan Adam da tallafawa al’umma ta Awareness for Human Right And Charity Foundation (AWRCF) ta gudanar da gangamin bayar da kyautar jini ga masu fama da lalurar Sikila a Asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake birnin Kano.
Da yake bayyana masudin gangamin a wannan rana shugaban kungiyar na kasa, Kwamaret Auwalu Usman Awareness ya ce sun shirya gangamin ne sakamakon korafin ƙarancin jini da Mata masu haihuwa da masu lalurar Sikila suke fuskanta a Asibitin
Jami’an Hukumar EFCC Sun Samu Nasarar Karɓe Kadara Mafi Girma Tun Bayan Kafa Hukumar
” Dama mun jima muna irin wannan aikin hakan ta sa muka tara mutane yan kungiyar mu da ma wadanda ba yan kungiyar mu ba, domin mu taimakawa bayin Allah da suke shiga cikin mawuyacin hali saboda ƙaranci jinin siyarwa da kuma waɗanda ma ba su da halin siya”. Kwamaret Auwalu Awareness
Ya ce tallafin jinin da suka bayar har kimanin leda dari da hamsin 150 ya kebanta ne kawai ga masu ciwon sikla da yara da kuma mata masu juna biyu.
Al’umma da dama ne dai suka halarci taron gangamin bayar da jini kyautar wadanda suka hadar da yan Kungiyar da wadanda ba ‘yan Kungiyar ba, duk domin tallafawa masu karamin karfi dake cikin al’umma
Commarade Auwal Usman ya shaidawa manema labarai cewa aiyukan kungiyar sun hadar da aiyukan jin kai da wayar da kan al’umma da kuma kare hakkin bil’adam.
Wasu daga cikin wadanda suka ba da tallafin jinin sun bayyana cewa sun bayar da jini kyauta ne domi domin marasa karfi cikin majinyata su amfana soboda Allah
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai6 days ago
An Kashe Mutane 418, An Yi Garkuwa Da 227 Cikin Watanni Biyu A Nijeriya — Rundunar Ƴansanda
