News
Jami’an Hukumar EFCC Sun Samu Nasarar Karɓe Kadara Mafi Girma Tun Bayan Kafa Hukumar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kotu ta sahalewa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta karɓe wani rukunin gidaje 731 dake birnin Abuja, daga wani tsohon ƙusa a cikin gwamnatin tarayya wanda hukumar ba ta bayyana sunansa ba.
Mai Shari’a Justice Jude Onwuegbuzie ne ya bayarda umurnin a cikin hukuncin da ya yanke a yau, a cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.
Ma’aikata A Kaduna Sun Fara Yajin Aiki Saboda Rashin Aiwatar Da Sabon Mafi Ƙarancin Albashi
Rukunin gidajen dake a yankin Cadastral Zone C09, Gundumar Lokogoma, a Abuja, a yanzu kotu ta hannunta su ga gwamnatin tarayya.
Ba a ambaci sunan mutumin da aka kwace kadarar daga hannunsa ba, amma Oyewale ya bayyana cewa kadarar na wani tsohon babban jami’in gwamnati ne.
“Matakin kwace wannan kadarar na karshe ya samo asali ne daga wani umarnin kwace na wucin gadi da aka samu a gaban wannan Alkalin a ranar 1 ga Nuwamba, 2024,” inji shi.
“Wannan jami’in gwamnati wanda ya mallaki kadarar ta hanyar zamba yana fuskantar bincike daga EFCC.
“A wannan lamari, Hukumar ta yi amfani da Sashe na 17 na Dokar Yaudarar Kuɗi da Sauran Laifukan Zamba mai lamba 14 ta shekarar 2006 da Sashe na 44 (2) B na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 wajen kare matsayarta.”
“Dokar Kafa Hukumar ta EFCC tana mai da hankali sosai kan dawo da kadarori.”
Mai magana da yawun EFCC ya ce alkalin ya yanke hukunci cewa wanda ake zargin ya kasa gabatar da hujja mai karfi da za ta hana a kwace kadarar.
Oyewale ya nakalto Ola Olukoyede, shugaban EFCC, yana cewa dawo da kadarori wata babbar hanya ce a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa da sauran laifukan tattalin arziki, kuma yana zama babban cikas ga masu aikata laifuka.
