Connect with us

News

Yawan Lafta Shafe-shafen Kwalliya Na ‘Yan Gayu Na Haddasa Cututtuka —Likitar Fata

Published

on

Yawan lafta shafe shafen kwalliya na ‘yan gayu na haddasa cututtuka irin su Hepatitis, Kyandan Biri da Kanjamau Gargadin Likitar fata

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Wata kwararriyar likitan fata dake aiki da babban asibitin koyarwa na gwamnatin jihar Legas Dr Folakemi Cole-Adeife ta bayyana cewa rashin tsaftace kayan shafe-shafen kwalliya kan haddasa cututtuka irin su Kyandan Biri, Hepatitis da Kanjamau.

Advertisement

Folakemi ta yi wannan kira ne yayin da take hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN,  a garin Legas a wannan mako.

Wani Mutum Shi Da Matarsa Sun Rasa Rayukansu Sanadiyar Gobara D Ta Tashi A Gidan Su A Kano

Likitar ta ce masu yi wa mutane kwaliya a mafi yawan lokuta basu tsaftace kayan shafe-shafensu kafin su yi wa wani aiki bayan su yi amfani da su a baya. Hakan ke sa sai ya debo wasu cututtukan dahga fatar wata a lafta wa wata.

Advertisement

Ta ce abinda ya fi kyau shine duk mace ta tanadi nata kayan kwalliyar duk lokacin da ta bukaci yin kwalliya sai ta mika wa mai yi kayanta ta yi mata da shi.

“Ana iya kamuwa da kwayoyin cututtukan fungi, bacteria ko viruses ta irin wannan hanyar.

Advertisement

A dalilin haka neke kira ga mutane da su rika kiyayewa tare da tabbatar da cewa masu kwaliya sun tsaftace kayan aikinsu da hanayen su kafin su fara aiki.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending