News
Ko Sama Da Kasa Za Su Hade Sai An Cigaba Da Rusau A Abuja —Nyesom Wike
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya sha alwashin ci gaba da rushe-rushe a Abuja duk da irin matsin lamba da yake sha.
A cigaba da aikn rushe rushe da minista Wike ke yi a kwanakin baya an ji wani kamfanin gine-gine mai suna Paullosa Nigeria Limited ya yi yekuwa game da sanarwa da hukumar raya babban birnin tarayya Abuja ta bayar na rusa masa gidaje a unguwar Lifecamp da ke Abuja.
Yawan Lafta Shafe-shafen Kwalliya Na ‘Yan Gayu Na Haddasa Cututtuka —Likitar Fata
Babban Manajan rukunin gidaje, Mista Vincent Enoghase, wanda ya zanta da manema labarai a Abuja ranar Talata, ya labarto cewa FCDA ta bukaci Naira miliyan 10, domin mallakar hakkin mallaka, ya ce sun biya amma har yanzu shiru basu samu sheda ba.
Sai dai a wani faifan bidiyo da ya saki a ranar Laraba, wani mai sharhi a kafafen sada zumunta, Vincent Martins Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, ya yi zargin cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, ya soke takardar mallakar gidajen,tare kuma da bayar da gidajen ga wani kamfanin Saravera Nigeria Limited, da kuma shugaban marasa rinjaye dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Obio/Akpor, Kingsley Chinda.
A nashi bangaren da yake magana a lokacin rabon motocin aiki ga jami’an tsaro a sakatariyar FCTA a jiya Alhamis, Wike ya ce gine-ginen da Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA) ke rushewa, gini ne da aka gina su a filayen gwamnati kuma ba bisa ka’ida ba.
