Connect with us

News

Wani Mutum Shi Da Matarsa Sun Rasa Rayukansu Sanadiyar Gobara D Ta Tashi A Gidan Su A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Sakamakon tashin gobara wani dattijo mai shekara 67, Muhammad Uba da matarsa mai suna Fatima Muhammad mai shekara 52 sun mutu a Kano.

Advertisement

Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’a a unguwar Rangaza (Inken) Layin AU da ke ƙaramar hukumar Ungogo a jihar.

Kamaru Ta Zamo Kasar Farko Da Ta Fara Sayen Man Dangote Daga Ketare

A cewar mai magana da yawun Hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusif Abdullahi, hukumar ta samu kiran agajin gaggawa da misalin ƙarfe 01:45 na tsakar dare daga ɗaya daga cikin ma’aikatan ta, FS Ahmad Abubakar ya sanar da faruwar gobarar.

Advertisement

Ya ce, “Ma’aikatan da ke bakin aiki daga ofishin kashe gobara na Bompai sun halarci zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka isa wurin da misalin ƙarfe 01:51 na tskar daren, da isar su sai suka ga an samu nasarar shawo kan gobarar.

“Wurin da gobarar ta tashi a wani ginin bene ne, amma gobarar ta tashi ne a ginin ƙasa wanda ake amfani da shi a matsayin gidan zama, mai ɗakuna biyu inda wutar ta cinye.

Advertisement

“A halin da ake ciki, Muhammad Uba da matarsa Fatima Muhammad, hayaƙin ne ya hana su fita, an kuɓutar da su a sume da raunin ƙuna a wasu sassan jikinsu, daga baya kuma aka tabbatar da mutuwarsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending