News
Sakataren Gwamnatin Bauchi Ya Yi Murabus
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya amince da murabus din Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Ibrahim Muhammad Kashim
Sanarwar hakan ya fito ne ta hannun mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Mukhtar M. Gidado, inda ya bayyana cewa murabus din ya fara aiki nan take.
Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa nan take aka umurci Dr. Aminu Hassan Gamawa, da ya karbi ragamar aikin na rikon kwarya.
A nashi bangaren Gwamnan jihar Bala Muhammed ya gode wa Barista Kashim bisa jajircewa wajen aiki da kuma kokarin cigaban jihar a lokacin da yake matsayin Sakataren Gwamnati .
Advertisements
