Connect with us

News

CNG: Gwamnatin Kano ta sanya hannu kan yarjejeniyar dala miliyan $15 

Published

on

IMG 20250124 WA0035

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA 

 

Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Kano, KANINVEST, ta rattaba hannu kan yarjejeniya (MoU) tare da STATA Power Utility Nigeria Limited don aiwatar da shirin iskar gas na musamman a jihar.

Da yake magana a wajen rattaba hannun yarjejeniyar a hedikwatar KANINVEST a Kano ranar Juma’a, Darakta Janar na hukumar, Muhammad Nazir Halliru, ya ce wannan yarjejeniya mai darajar dala miliyan $15 wani muhimmin ci gaba ne wajen samar da yanayi mai kyau ta hanyar rage hayakin gurbata muhalli, samar da tsabta da kuma kirkirar damarmakin ayyukan yi.

Zamu Ƙara Tsaurara Matakan Tsaro Kan Yiwuwar Harin Ta’addaci A Kano

A cewarsa, idan aka aiwatar da shirin, zai kunshi samar da iskar Compressed Natural Gas (CNG) da kuma sauya motocin da ke amfani da man fetur zuwa amfani da iskar gas.

Mr. Halliru ya bayyana cewa wannan yunkuri zai taimaka wajen magance matsalolin hauhawar farashin mai da kuma wahalhalun sufuri a wannan jihar da ke cike da kasuwanci.

Advertisement

“Wannan yana nuna hangen nesa na wannan gwamnati wajen samar da yanayi mai kyau ta hanyar rage hayakin gurbata muhalli, kiyaye tsabta, da kuma samar da ayyukan yi.

“Samar da iskar gas din ba zai tsaya ga motocin ba kawai, har ma zai fadada zuwa masana’antu da manyan kamfanoni da ke amfani da CNG ko kuma za su iya fara amfani da shi domin bunkasa samar da kayayyaki da ayyukansu,” inji shi.

Darakta Janar ya bayyana cewa za a fara aiwatar da hadin gwiwar nan cikin watanni shida, bayan da kamfanin ya kafa tashoshin iskar gas a jihar.

“Mun samu amincewar mai girma Gwamnan Jihar akan wannan babbar jarin. Muna sa ran aiwatarwa zai fara cikin watanni shida masu zuwa idan suka kammala gina tashoshin su da wuraren da aka riga aka basu izini.

“Suna kuma da kariya ta musamman na rangwamen haraji kasancewar wannan jarin ne na farko,” ya bayyana.

A bangarensa, Shugaban Kamfanin STATA, Salman Dantata, ya bayyana farin cikin sa kan wannan yarjejeniya mai muhimmanci wadda a cewarsa, za ta taimaka wajen rage farashin sufuri da bunkasa masana’antu a Kano.

Advertisement

“Wannan tsari yana daidai da al’adun duniya na amfani da makamashi mai tsafta, bunkasar tattalin arziki, da kuma dorewar muhalli.

“Ta hanyar sauyawa daga amfani da man fetur zuwa Compressed Natural Gas (CNG) a motocin sufuri, wannan shiri zai rage farashin sufuri, inganta ingancin iska, rage hayakin carbon, da kuma karfafa amfani da makamashi mai inganci a fadin Jihar Kano,” inji shi.

Mr. Dantata ya bayyana cewa zuba jarin zai kai dala miliyan $15 daga STATA cikin shekaru biyu don samar da tashoshin LCNG a fadin jihar.

Ya ce kamfanin zai saka jari wajen kayan sauyawa da kafa cibiyar sauya tsarin amfani da gas a cikin tashoshin.

Ya kara da cewa cikin shekara guda, za su fara samar da keke-napep 5,000 masu amfani da hasken rana da kuma motoci 10 na sufuri don amfanin kasuwanci a jihar.

Mr. Dantata ya ce za a kafa babbar tashar a yankin Tamburawa na karamar hukumar Kura, tare da karfin samar da metric ton 110 a rana.

Advertisement

Sauran tashoshin gas masu karfin metric ton 2 kowanne za a kafa su a Dalladi Nasidi, Maiduguri Road, IBB Road, Shagari Quarters, Cotton Gingery, Sharada, da Bechi Quarters.

Ya bayyana cewa kamfanin na da shirin fadada zuwa tashoshi 20 cikin shekaru biyar, wanda zai samar da ayyuka sama da 300 kai tsaye da kuma ayyuka 5,000 na kai tsaye ga matasan jihar Kano, wacce ita ce jihata biyu mafi yawan jama’a a kasar.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending