News
Zamu Ƙara Tsaurara Matakan Tsaro Kan Yiwuwar Harin Ta’addaci A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta gargadi mazauna jihar kano kan rahotannin sirri da ke nuna yiwuwar wani shiri na ‘yan ta’adda don kai hari a wuraren taruwar jama’a da wurare masu muhimmanci a fadin jihar.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sa hannu, an bukaci mazauna jihar su kasance masu takatsantsan tare da kauce wa wuraren cunkoson jama’a har sai wani karin bayani ya biyo baya, domin bai wa hukumomin tsaro damar gano da kuma dakile duk wata barazana.
Gwamnatin Kano Ta Sauya Ranar Da Za’a Gudanar Da Tsaftar Muhallin Na Janairu
Sanarwar ta ce: “runduanar ‘Yan Sandan Jihar Kano tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun sami rahoton sirri na cewa akwai wani shiri na ‘yan ta’adda don kai hare-hare a wuraren taruwar jama’a a wurare masu muhimmanci a fadin Jihar Kano.
“Don haka, muna kira ga mazauna jihar da su kasance masu takatsantsan tare da kauce wa wuraren da ake cunkoso har sai wani karin bayani domin bai wa jami’an tsaro damar gano da kuma dakile duk wani mai yiwuwar kai hari.”
Sanarwar ta kara da cewa, domin magance wannan barazana, rundunar ta tura ƙwararru daga sashin binciken abubuwan fashewa (EOD) da kuma sassan Chemical, Biological, Radiological, and Nuclear zuwa wurare masu muhimmanci a fadin jihar. An tsare ƙungiyoyin a cikin shirin ko-ta-kwana kuma za a iya tuntuɓar su ta lambobin 08169884988 ko 07067157218 don bayar da rahoto kan duk wani mutum ko abu da ake zargi.
Haka kuma, an bukaci mazauna jihar da su rika kai rahoton gaggawa ko duk wani abu da ba a saba gani ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma tuntubar rundunar kai tsaye ta lambobin gaggawa: 08032419754, 08123821575, ko 09029292926.
SP Kiyawa ya jaddada cewa lura da tsaro daga jama’a da kuma haɗin kai suna da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro da kuma hana faruwar duk wani lamari.
Daga karshe, rundunar ta yi kira ga mazauna jihar da su kasance cikin natsuwa tare da lura da duk wani abu da ake zargi da kuma bin duk wasu ka’idojin tsaro yayin da ake kan kokarin hana duk wani yiwuwar hari.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
