News
Gwamnatin Kano Ta Sauya Ranar Da Za’a Gudanar Da Tsaftar Muhallin Na Janairu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Kano ta ce an Sauya lokacin Tsaftar Muhallin da ake Gudanarwa a duk juma’a da Asabar din karshen wata ta Watan Janairun 2025 zuwa mako mai zuwa.
Daraktan yada labarai na maaikatar Muhalli da yaki da sauyin yanayi na jihar Kano Malam Ismail Garba Gwammaja ne ya sanar da hakan a madadin kwamishinan ma’aikatar Dakta Dahiru Muhammad Hashim kamar yanda Jaridar GLOBAL TRACKER ta ruwaito
Idan Za’a iya tunawa a shekarun baya ana gudanar da Tsaftar Muhallin a duk juma’a da Asabar din karshen wata koda kuwa ranakun sun sami bambancin mako kamar yadda aka samu a wannan lokacin, Amma a wannan lokacin sai kwamishinan Ya bada umarnin gudanar da Tsaftar Muhallin a mako mai zuwa wanda juma’a zata kasance 31 ga Watan Janairu yayin da Asabar zata kasance 1 ga Watan Fabarairun 2025.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
