Connect with us

News

EL-RUFAI YA SHIGA RIKICIN RIBADU / NAJA’ATU  : Ribadu Na Fama Da Matsananciyar Cutar Mantuwa

Published

on

FB IMG 1738760635790

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya shiga cacar baki tsakanin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da Hajiya Naja’atu Muhammad, tsohuwar kwamishiniyar hukumar ‘yan sanda ta PSC.

Advertisement

DAILY TRUST ta ruwaito cewa Takardun bayanan zaman Majalisar Dattawa za su tabbatar da cewa Nuhu ya furta wadannan kalmomi a wani lokaci a shekarar 2006.

A rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa a watan Fabrairun 2007 ya sake tabbatar da muhimman wadannan bayanan kalmomi.

Advertisement

Gobara Ta Yi Sanadiyar Rasa Rayuka Da Dukiya A Makarantar Allo A Kauran Namoda

Shawarar da Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta yanke a shekarar 2006—wanda za a iya samu daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF)—na dauke da wadannan zarge-zarge.

A wannan taron majalisar zartarwa FEC

Advertisement

Idan za iya tunawa, ‘Yar gwagwarmaya Hajia Naja’atu tace ko gezau bazata bada haƙurin ba

Ƴar gwagwarmaya kuma ƴar siyasa, Naja’tu Mohammed, ta shaidawa mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Nuhu Ribadu, cewa ba za ta bashi haƙuri ba, in ya so ya garzaya kotu kan kalaman da ya ce ta yi masa.

Advertisement

Naj’atu ta ce, Ribadu ya taba bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin mai cin hanci da rashawa amma kuma gashi ya na da mukami a gwamnatin ta Tinubu a matsayin NSA.

Daga nan ne sai Ribadu ya nemi da Naja’atu ta janye kalaman nata a kan ta kuma fito ta bashi haƙuri.

Advertisement

A wata hira ta wayar tarho da gidan REDIYON PREMIER a jiya Talata da yamma, Naja’atu ta ce ta tsaya tsayin daka kan abin da ta fada game da Ribadu, inda ta kalubalance shi da ya kai ta har zuwa Kotun Ƙoli.

“A matsayinsa na shugaban EFCC, Ribadu ya taba cewa Tinubu na cikin wadanda suka fi cin hanci da rashawa. Kuma a cikin gwamnonin Najeriya, Tinubu na daya ne.

Advertisement

“Bidiyon yana kan Youtube, kuma a kan wannan batu, ba zan janye ba. Ina kan baka ta,” in ji ta

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending