News
Gobara Ta Yi Sanadiyar Rasa Rayuka Da Dukiya A Makarantar Allo A Kauran Namoda
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wata gobara mai muni ta tashi a wata makarantar Allo ta Malam Muhammadu Ghali da ke bakin kasuwa, a garin Kauran Namoda, jihar Zamfara, lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa A daren jiya Talata,.
Wani mazaunin garin, Musa Sani Musa, ya shaidawa DALA FM, cewa gobarar ta yi sanadiyar rasuwar almajirai 17, yayin da wasu yara 12 suka jikkata kuma a halin yanzu suna karbar magani a asibiti.
Har zuwa yanzu, ba a bayyana hakikanin abin da ya haddasa gobarar ba, sai dai ana ci gaba da bincike don gano musabbabinta. Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta yi matukar muni, inda ta lashe dakunan kwanan almajirai tare da dukiyoyinsu.
Jama’ar gari da hukumomi sun bayyana alhinin su kan wannan mummunan lamari, tare da kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su dauki matakan da suka dace don kare irin wannan hadari a nan gaba.
