News
Shugaba Tinubu Ya Tafi Faransa
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tafi Faransa gabanin taron ƙasashen Afrika
Tinubu zai shafe mako guda a Faransa, inda daga nan zai wuce taron ƙungiyar ƙasashen Afrika AU, da zai gudana tsakanin 12 zuwa 16 ga watan Fabrairu a birnin Addis Ababa na Habasha.
Mai Ba Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Bayani da Tsara Dab’i, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Ya ce tafiyar Shugaban Kasa zuwa kasar Turai na da dalilai na kashin kansa, tare da bayyana cewa ziyarar ta kasance ne a hanyarsa zuwa Addis Ababa, babbar birnin Habasha.
Mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana cewa Tinubu zai isa Addis Ababa farkon mako mai zuwa don taron koli na Kungiyar Tarayya.
Details soon
Advertisements
