Connect with us

News

NiMet Ta Yi Hasashen Faduwar Damuna Da Wuri A Wasu Jihohin 

Published

on

Damuna

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMet) ta bayyana cewa za a fuskanci faduwar damuna da wuri a wasu jihohi, yayin da wasu za su fuskanci jinkirin ruwan sama a farkon shekarar 2025.

Advertisement

A cikin hasashen yanayi da ta fitar, hukumar ta ce jihohin Legas, Ogun, Delta, Rivers, da wasu jihohi tara za su fara fuskantar ruwan sama da wuri. Haka zalika, jihohin Arewa guda takwas da suka hada da Plateau, Kaduna, Niger, Benue, Nasarawa, Taraba, Adamawa, da Kwara za su fuskanci jinkirin ruwan sama.

Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Saboda Kasa Jurewa Matsin Rayuwa Da Yake Fuskanta

NiMet ta bayyana cewa jihohin Delta, Bayelsa, Rivers, Anambra, da wasu yankunan Oyo, Ogun, Osun, Ondo, Legas, Edo, Enugu, Imo, da Ebonyi za su fara samun saukar ruwan sama da wuri.

Advertisement

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo SAN, ne ya gabatar da wannan hasashen na shekarar 2025 a birnin Abuja. Hukumar ta kuma yi hasashen cewa ana sa ran damuna za ta sauka a yankunan Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom, da wasu sassan Delta tsakanin 23 ga watan Fabrairu zuwa 10 ga watan Maris.

Hukumar ta shawarci manoma, hukumomin kula da ambaliya, da sauran masu ruwa da tsaki su dauki matakan da suka dace domin shirin fuskantar yanayin daminar bana.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending