News
Dubban ‘Yan Jumhuriyar Nijer Sun Tare A Harabar Sansanin Sojan Faransa Da Ke Yamai
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dubban mazauna birnin Yamai sun fara zaman dirshan na sai yadda hali ya yi a harabar sansanin sojan Faransa da zummar tilasta wa gwamnatin shugaba Macron kwashe wadannan sojoji daga kasar ta Nijer.
A yayin da a yau Asabar 2 ga watan Satumba ya kamata dakarun Faransa 1500 masu yaki da ta’addanci su dakatar da ayyukansu a Jamhuriyar Nijer kamar yadda sojojin juyin mulkin kasar suka ba su wa’adin wata 1, dubban mazaunan birnin Yamai sun fara zaman dirshan na sai yadda hali ya yi a harabar sansanin sojan na Faransa da zummar tilasta wa gwamnatin shugaba Macron kwashe wadannan sojoji daga kasar ta Nijer.
Kungiyar Likitoci A Kogi Sun Shirya Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Yanayin tsamin dangataka a tsakanin kasashen 2 ya samo asali a washegarin juyin mulkin da sojoji suka yi wa zabebben shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.