News
Man Fetur Zai Sauko Zuwa Ƙasa Da N200 a Kowace Lita Idan Aka Gyara Matatu, -IPMAN
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban ƙungiyar daillalan man fetur masu zaman kansu IPMAN ya ce ‘yan Najeriya zasu iya sayen fetur kan N200 a kowace lita Joseph Obele, shugaban IPMAN na jihar Ribas ya ce hakan zata faru ne idan FG ta gyara matatun man cikin gida suka ci gaba da aiki Ya ce amma idan haka bata samu ba, farashin fetur zai ci gaba da ƙaruwa sakamakon canjin yanayin kasuwa.
Shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar man futur masu zaman kansu reshen jihar Ribas, Joseph Obele, ya roƙi gwamnatin tarayya ta tabbatar da an gyara matatun man cikin gida. Ya bayyana cewa farashin man PMS wanda aka fi sani da Fetur zai sauko ya dawo ƙasa da Naira 200 kan kowace Lita idan matatun man Najeriya suka ci gaba da aiki.
Dubban ‘Yan Jumhuriyar Nijer Sun Tare A Harabar Sansanin Sojan Faransa Da Ke Yamai
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da biyan tallafin man fetur, wanda ya haddasa tashin farashin litar mai da tsadar rayuwa. Domin farfaɗo da tattalin arziƙin kasa, shugaba Tinubu ya yi alƙawarin tabbatar da matatar man Patakwal ta fara tace ɗanyen mai a watan Disamba, 2023.
Sai dai Obele, a wata hira da ya yi da jaridar Punch ranar Asabar, ya nuna damuwarsa kan yadda karancin dala ke ci gaba da shafar masu shigo da kaya. Ya kara da cewa farashin fetur zai ci gaba da karuwa idan gwamnati ta kasa lalubo mafita cikin ƙanƙanin lokaci, jaridar Ripples ta tattaro.
A kalamansa, shugaban IPMAN ya ce: “Matuƙar matatun mai na kasarmu ba su aiki, farashin lita zai ci gaba da karuwa saboda canjin yanayi. Amma idan matatun mu suka fara aiki, ‘yan Najeriya za su sayi mai kasa da Naira 200 kan kowace lita.” “Ƙarancin dala ya sa da wahala masu shigo da man fetur su ci gaba da shigo da shi daga waje. Kimanin makonni biyu ke nan ana cikin wannan yanayi.”
