News
Hukumar Hisbah Ta Kama Shagon Siyar Da Giya A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jami’an hukumar Hisbah sun kai samame zuwa wani shago da ke kan titin Ibo Road, kusa da France Road, inda aka kama ana siyar da giya duk da haramcin da aka sanya a baya.
Wannan shago an kama shi tun a shekarar 2024, amma bayan samun rahoton cewa ba su daina kasuwancin ba, jami’an hukumar suka sake kai farmaki da misalin karfe 4:45 na yamma. A wannan samamen, an samu nasarar kwashe katako 115 na giya.
Gwamantin Kano Za Ta Zuba Jari A Fasahar Artificial Intelligence AI
Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Abubakar, ya tabbatar da kamen, yana mai jaddada cewa za a dauki matakan doka kan masu karya dokokin hana safarar giya a yankin.
Hukumar ta yi gargadi ga duk masu aikata irin wannan laifi da su dakata, domin za a ci gaba da gudanar da bincike da kama duk wanda aka samu da
laifi.
