Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Kudirinta na Kawar da Cutar Tarin Fuka Nan Da Shekarar 2030

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamnatin Jihar Kano ta sake nanata kudirinta na yaki da cutar tarin fuka (TB) tare da tabbatar da kawar da ita gaba daya nan da shekarar 2030.

Advertisement

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Cibiyar Ayyukan Gaggawa na Lafiya (EOC), Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase.

Kotu Ta Bada Damar Yin Kiranye Ga Sanata Natasha

A cewarsa, cutar TB na ci gaba da yin barna a duniya, inda rahotanni suka nuna cewa mutane miliyan 10.6 sun kamu da cutar a shekarar da ta gabata. Najeriya ce ta daya a Afirka kuma ta shida a duniya dangane da yawan masu dauke da cutar, yayin da Kano ke daga cikin jihohin da ke da mafi yawan masu TB a kasar.

Advertisement

A shekarar 2024 kadai, Kano ta samu rahoton mutane 33,690 da suka kamu da cutar, daga cikinsu 28,169 sun samu kulawa da magani, adadi mafi girma da kowace jiha a Najeriya ta taba cimmawa.

Gwamnatin Kano ta dauki matakai masu karfi domin dakile cutar, ciki har da:

Advertisement

Samar da fiye da 1,391 na’urorin kula da masu TB (DOTS sites) da fiye da 300 dakunan gwaji.

Shigar da sabbin wuraren gwaji a makarantu, sansanonin soja, gidajen yari, da sauran wurare.

Advertisement

Karfafa hadin gwiwa da kungiyoyin farar hula, kafafen yada labarai, da shugabannin addini.

Kwamishinan ya bukaci al’umma da su rika zuwa cibiyoyin lafiya domin samun gwaji da magani kyauta, tare da gode wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da yake bai wa bangaren lafiya.

Advertisement

Ya kuma yaba da rawar da sarakunan gargajiya, kungiyoyin addini, da kungiyoyin agaji kamar WHO, UNICEF, da Aliko Dangote Foundation ke takawa a yaki da cutar.

A karshe, ya bukaci daukacin al’umma su hada hannu domin cimma burin kawar da cutar TB nan da shekarar 2030.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending