News
Kotu Ta Bada Damar Yin Kiranye Ga Sanata Natasha
Babbar Kotun Tarayya dake Lokoja, Jihar Kogi, ta yanke hukuncin cewa Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) na da damar karɓar bukatar yin kiranye da al’ummar mazaɓar Kogi ta Tsakiya suka gabatar akan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
A hukuncin da aka yanke a ranar Juma’a, kotun ta tabbatar da cewa yin kiranye abu ne da doka ta amince da shi, don haka al’umma na da ‘yancin aiwatar da bukatarsu cikin lumana da bin doka.
Kotun ta kuma yi gargadi ga INEC da jami’anta kan karɓar korafe-korafen da ke dauke da sanya hannu na bogi ko kuma yin hukunci a kansu ba tare da bin ka’idar doka ba.
An dage sauraron ƙarar zuwa ranar 6 ga watan Mayu, 2025, inda za a ci gaba da tantance sahihancin bukatar kiranyen.
Advertisements
