News
Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Akpabio Kan Dakatar Da Sanata Natasha
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta kori ƙorafe-ƙorafen da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya shigar dangane da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar dattawa.
A zaman kotun da aka yi ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka, kotun ta amince da buƙatar Akpabio na janye ƙorafe-ƙorafen da ya shigar a ranar 20 da kuma 25 ga watan Maris, 2025.
Sai dai kotun ta kori ƙorafe-ƙorafen baki ɗaya tare da umartar Sanata Akpabio da ya biya tarar Naira 100,000 ga Sanata Natasha a matsayin diyya bisa ɓata mata lokaci.
Haka kuma, kotun ta bayar da umarnin goge lambar ƙarar daga cikin kundin shari’a, abin da ke nufin ƙarshen shari’ar a matakin kotun ɗaukaka ƙara.
Sanata Akpabio ya shigar da buƙatar ne yana neman kotu ta ba shi lokaci da damar ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 10 ga watan Maris, 2025.
A cikin wannan shari’ar, Sanata Natasha ce ta maka Shugaban Majalisar Dattawa, da wasu mutane uku a gaban kotu kan dakatar da ita daga kujerarta.
Akpabio ya nemi kotu ta dakatar da ci gaba da sauraron karar a babbar kotu har sai an yanke hukunci a kotun ɗaukaka ƙara, amma bayan janyewar ƙorafin, kotun ta ce babu ci gaba da sauraron buƙatun nasa.
