Connect with us

News

“Kannywood Ta Ba Ni Cikakken Goyon Baya —Prince Daniel (ABOKI), Daraktan Mai Martaba”

Published

on

IMG 20250325 WA0030 (1)

Babban daraktan fim ɗin Mai Martaba, Prince Daniel (ABOKI), ya bayyana cewa masana’antar Kannywood ba ta nuna masa wariya ba dangane da kabilanci ko addini, illa ma goyon baya da ƙwararrun masana’antar suka ba shi.

Prince Daniel ya yi wannan bayani ne domin fayyace rahotannin da suka yadu kwanan nan cewa masana’antar Kannywood ta ƙi amincewa da shi, haka kuma Nollywood na nuna masa bambanci saboda yana ɗan Arewa. A cewarsa, waɗannan labarai ba su da tushe.

Advertisement

Fubara Ya Musanta Zargin Yana Da Hannu A Hare-haren Da Ake Kai Wa Bututun Mai

“Na halarci wani taro na masana’antar Nollywood da Hollywood a birnin Los Angeles, inda na yi bayani kan ƙalubalen da muka fuskanta yayin yin fim ɗin Mai Martaba da yunƙurin kai shi ga matakin kambun fina-finai na duniya, Oscars. A wannan taro ne na ambaci matsalolin da muke fuskanta a Najeriya, ciki har da rashin tsaro da kuma wahalar samun tallafin kuɗi.”

Ya ƙara da cewa: “Na yi wannan bayanin ne da kyakkyawar niyya domin masu sauraro su fahimci yadda masana’antar fina-finai ke aiki a Najeriya. Amma an yi wa maganata gurguwar fahimta.”

Advertisement

Prince Daniel ya jaddada cewa Kannywood ta ba shi cikakken goyon baya, kuma yana alfahari da kasancewarsa ɗan Kannywood da ke zaune a Kano, inda yake gudanar da harkokinsa.

“A yau, ina alfahari da kasancewa ɗan fim daga Arewa, kuma na samu goyon baya daga masana’antar ba tare da nuna bambanci ba. Saboda haka, zan ci gaba da hada kai da takwarorina domin daukaka martabar masana’antar Kannywood, fadakar da duniya kan labaranmu na gaskiya, da kuma samar da guraben aikin yi ga matasa.”

Advertisement

Fim ɗin Mai Martaba dai na ɗaya daga cikin manyan fina-finan da ke fatan wakiltar Najeriya a gasar fina-finai ta duniya, kuma yana ci gaba da jan hankalin masu kallo a ciki da wajen ƙasa.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending