News
An Rotsa Babura 601 A Abuja 601 A Abuja
A ci gaba da kokarin dakile amfani da babura a sassan Babban Birnin Tarayya da ke fama da cunkoso da rashin tsaro, Hukumar gudanarwar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta lalata babura guda 601 da aka kama bisa karya dokar hana zirga-zirgar su.
Lalata wadannan babura ya gudana ne ranar Talata karkashin kulawar Hukumar Kula da Harkokin Motoci da Zirga-zirga (DRTS), a karkashin jagorancin Ministan Abuja, Nyesom Wike. Wannan mataki ya biyo bayan aiwatar da dokar da ke hana amfani da babura a wasu yankuna na birnin, wanda aka fara tun 1 ga Janairu, 2023.
Jam’iyyun Siyasa A Najeriya Ba Su Da Alkibla – Kakakin Majalisa Abbas
Sakataren harkokin sufuri na FCTA, Dakta Elechi Chinedum, ya bayyana cewa wannan aiki yana da nasaba da doka da gwamnatin da ta gabata karkashin tsohon Minista, Mohammed Bello, ta shimfida domin kiyaye doka da oda a birnin.
”Dokar ta kayyade wuraren da ba a amince a rika amfani da babura ba, kuma abin da muka yi yau wata hanya ce ta tabbatar da cikar wannan doka,” in ji Dakta Chinedum.
A nasa jawabin, shugaban DRTS, Dakta Abdulateef Bello, ya bayyana cewa haramcin babura a babban birnin ba sabon abu ba ne, domin tun daga shekarar 2006 aka fara daukar matakin. Ya ce babura suna haddasa cunkoso, hadurra da kuma taimakawa aikata laifuka.
”Wannan aiki wata hanya ce ta kara tabbatar da haramcin babura a cikin birnin tarayya. Muna gargadin masu zuba jari a harkar babura da su dakatar da hakan, domin gwamnati za ta ci gaba da kwace su tare da lalata su kamar yadda kotu ta bayar da umarni,” in ji shi.
Shi ma jami’in ‘yan sanda mai kula da ayyuka a rundunar FCT, ACP Mode Magawata, ya bayyana damuwa kan yadda ake amfani da babura wajen aikata laifuka kamar fashi da makami da kuma satar mutane.
”Minista ya bada umarni cewa babu babura a yankunan da aka haramta, kuma mu a hukumance muna tabbatar da bin wannan umarni,” in ji ACP Magawata.
Wannan mataki na kara nuna kudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaro da daidaito a harkokin zirga-zirga a Babban Birnin Tarayya.
LEADSHIP
