News
Jam’iyyun Siyasa A Najeriya Ba Su Da Alkibla – Kakakin Majalisa Abbas
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa a Najeriya ba su da tsayayyun manufofi da alkibla, yana mai zargin cewa yawancin su ba sa aiki da kishin kasa ko ra’ayin dimokuraɗiyya.
A wani taro da aka gudanar a Abuja kan dokar jam’iyyun siyasa tare da haɗin gwiwar ECES, YIAGA Africa da Cibiyar Kukah, Abbas – wanda wakilinsa Ishaya Lalu ya halarta – ya jaddada cewa lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su nemi sauyi daga shugabannin siyasa da jam’iyyun su.
Jami’an Hukumar EFCC Sun Kama Ma’aikacin Jirgi Da Abokinsa Kan Makudan Kuɗaɗen Waje A Kano
Ya kwatanta tsarin Najeriya da na kasashe irin su Amurka, Birtaniya da Sweden, inda hukumomi ke sa ido sosai kan harkokin siyasa. Ya ce a Amurka, hukumar FEC ce ke lura da kuɗaɗen kamfe da rajistar jam’iyyun siyasa, yayin da a Najeriya masu kuɗi ke ɗaukar nauyin jam’iyyun don cimma burinsu na kashin kai.
Abbas ya nuna damuwa kan yadda ‘yan siyasa ke sauya jam’iyya daga lokaci zuwa lokaci ba tare da tsayayyen akida ba, yana mai cewa hakan na janyo tabarbarewar siyasa da rashin amana ga jama’a.
Ya bayyana cewa Majalisa na duba wani kudiri da zai kafa hukuma mai zaman kanta domin lura da rajista da kudaden jam’iyyu siyasa – matakin da zai kawo gaskiya da daidaito a fagen siyasa.
Shugaban kwamitin jam’iyyun siyasa na Majalisa, Zakari Nyampa, ya ce dokar za ta kawo sauyi mai amfani tare da inganta gaskiya da amana a harkokin siyasa a Najeriya.
