News
Jam’iyyun Siyasa Na Daya Daga Cikin Manyan Matsalolin Da Ke Addabar Najeriya – Oby Ezekwesili
Tsohuwar Ministar Ilimi a Najeriya, Obiageli Ezekwesili, ta bayyana cewa jam’iyyun siyasa na daya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar kasar.
Ezekwesili ta yi wannan bayani ne a lokacin da take tsokaci kan yawan sauya sheƙa da ake yi daga wasu jam’iyyu zuwa jam’iyyar APC. Ta bayyana cewa irin wannan sauya sheƙa ba zai iya warware manyan matsalolin da Najeriya ke fama da su ba.
Gwamnati Ta Shirya Dakile Amfani Da Itace wajen Girki A Najeriya
A cewarta, “Zan iya gaya muku cewa jam’iyyun siyasa sun kasance cikin matsalolin gazawar ‘yan elit dinmu, domin kuwa ba mu taɓa samun jam’iyyun siyasa na hakika a Najeriya ba. Abin da muke da shi kawai jam’iyyun suna ne, ba tare da manufar gina kasa ba.”
Tsohuwar Ministar ta ce Najeriya ta dogara ne da tushen da bai da karfi, inda ta kwatanta tsarin sauya jam’iyya da kawai sauya “acronym” mara tasiri.
”Har yanzu ba mu kafa jam’iyyun siyasa masu inganci da za su dauki nauyin gina kasa ba. Idan aka tambaye ku abin da ke hada ku, kuma kuka ce APC, zan iya fada muku cewa abinda ke faruwa shi ne kawai canjin wadanda ke son rike ikon sarrafa komai,” inji ta.
Ezekwesili ta kammala da cewa gina kasa a bisa kuskuren tushe yana bukatar gyara na hakika. “Idan kana da matsalar tsarin gini, mafita mafi sauki ita ce ka nemo yadda za ka gyara tsarin gaba daya,” ta jaddada.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
