News
Wasu Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sake Kai Hari A Karamar Hukumar Shanono A Dake Kano
Rahotanni daga karamar hukumar Shanono a jihar Kano sun tabbatar da cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari a garin Shanono da daren Asabar, inda suka yi yunkurin sace wani attajiri tare da ‘ya’yansa guda biyu
PREMIER RADIO ta ruwaito cewa shaidu sun bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun shigo garin dauke da muggan makamai, ciki har da bindigogi, inda suka tsinke tsakar dare da harbe-harben bindiga a kusa da gidan attajirin.
Jam’iyyun Siyasa Na Daya Daga Cikin Manyan Matsalolin Da Ke Addabar Najeriya – Oby Ezekwesili
Wani mazaunin yankin ya ce: “Mun farka da karar bindiga, sai muka ga ana kokarin fitar da wani mutum tare da ‘ya’yansa biyu daga gidansu.”
Sai dai, a cewar rahotanni, attajirin da ‘ya’yansa sun samu nasarar kubucewa daga hannun masu garkuwa da mutanen, duk da cewar daya daga cikin wadanda aka yi yunkurin sacewa ya samu raunika, inda aka garzaya da shi zuwa asibiti domin samun kulawa.
Wannan lamari na baya-bayan nan na zuwa ne bayan wasu makamantan hare-hare da aka samu a garin, ciki har da sace wani mutum a kasuwar Shanono a kwanakin baya.
Hukumomi sun ce suna ci gaba da bincike tare da daukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama
