Connect with us

News

NUJ Ta Kaddamar Da Sabuwar Kungiyar Yan Jaridun Yanar Gizo A Kano 

Published

on

online
Comrade Abubakar Dangambo ya zama sabon Shugaba

Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin tallafa wa Ƙungiyar ‘Yan Jaridar Yanar Gizo domin ƙarfafa aikin yada sahihan labarai da kuma taimakawa ci gaban al’umma.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a yayin taron rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar, wanda aka gudanar a sakatariyar Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) reshen Kano.

‎Wasu Masu Garkuwa Da Mutane Sun Sake Kai Hari A Karamar Hukumar Shanono A  Dake Kano  ‎

A cewar Kwamishina Waiya, kafafen yada labarai na yanar gizo sun zama muhimmin abin dogaro wajen watsa bayanai a wannan zamani, inda ya bukaci sabbin shugabannin da su jajirce wajen tabbatar da ingantattun bayanai da kare martabar aikin jarida.

Shugaban kwamitin ƙaddamar da ƙungiyar, Alhaji Ahmad Aminu, ya bukaci ‘yan jarida na yanar gizo da su rika tantance gaskiyar labarai kafin wallafawa domin kauce wa yada labaran ƙarya da kan haifar da rikici. Ya kuma yaba wa gwamnatin Kano bisa ƙoƙarinta na inganta harkar labarai a jihar.

Sabon shugaban ƙungiyar, Comrade Abubakar Dangambo, ya bayyana kudurinsa na hada kai da sauran mambobi domin kare martabar aikin jarida da kuma tallafa wa cigaban jihar Kano. Ya ce za su yi aiki tukuru wajen tabbatar da sahihancin bayanai da wayar da kan al’umma cikin gaskiya da rikon amana.

Sauran sabbin shugabannin da aka rantsar sun hada da Khadijah Aminu a matsayin Mataimakiyar Shugaba, Isyaku Ahmad a matsayin Sakataren Ƙungiya, Zahara’u Nasir a matsayin Mataimakiyar Sakatariya, Abbas Yusha’u a matsayin Ma’ajin Kuɗi, da Zainab Bello a matsayin Mataimakiyar Ma’aji.

Advertisement

Taron rantsarwar ya samu halartar dimbin ‘yan jarida daga fadin jihar Kano, tare da nuna goyon baya da fatan alheri ga sabbin shugabannin da suka hau karagar mulki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending