News
NUJ Za Ta Karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf Da Lambar Girmamawa
Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa (NUJ), ƙarƙashin jagorancin, Kwamared Alhassan Yahaya, ta bayyana Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a matsayin ɗaya daga cikin fitattun shugabanni da za a karrama da lambar yabo ta musamman a bikin cika shekara 70 da kafuwar ƙungiyar.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta fitar, an bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu wannan lambar yabo ta “Media Friendly Award” ne saboda irin gudummawar da yake bayarwa wajen bunƙasa harkokin cigaban ƙasa, ƙarfafa shugabanci na gaskiya da adalci, da kuma goyon baya mara yankewa ga walwalar ‘yan jarida da ‘yancin fadar albarkacin baki a Najeriya.
Kotu Ta Ba Da Belin Emefiele Tsohon Gwamnan Cbn Kan Naira Biliyan 2
Sanarwar ta kara da cewa: “NUJ ta yi la’akari da irin jagorancin kwarai da Gwamna Yusuf ke yi wanda ke nuna kishin al’umma da goyon bayan harkokin yaɗa labarai, wanda hakan ya sanya hukumar ta bayyana shi a matsayin gwarzon shugaba da ya cancanci wannan lambar yabo.”
Za a miƙa lambar girmamawar a wani gagarumin taron girmamawa da za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga Yuni, 2025, a babban dakin taro na NUJ da ke birnin tarayya Abuja.
Da yake mayar da martani kan wannan kyauta, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana jin daɗinta bisa wannan matsayi da Gwamnan Jihar ya samu.
Ya kuma jaddada kudurin Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da mutunta ‘yancin kafafen yaɗa labarai da kare ‘yancin fadar albarkacin baki a matsayin ginshiƙin dimokuraɗiyya
