News
Kotu Ta Ba Da Belin Emefiele Tsohon Gwamnan Cbn Kan Naira Biliyan 2
Babbar Kotun Jiha da ke Maitama a Abuja, ta bayar da belin tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele Naira biliyan biyu bisa tuhumar mallakar gidaje 753 da ke yankin Lokogoma na babban birnin tarayya.
An gurfanar da Emefiele a gaban Mai Shari’a Yusuf Halilu a ranar Litinin, inda hukumar EFCC ta shigar da kara mai dauke da tuhuma takwas a kansa, dangane da kadarori da ake zargin an mallaka ta haramtacciyar hanya.
IFTILA’IN: Guguwa Mai Ƙarfi Ta Ruguza Sama da Gidaje 450 A Bauch
Sai dai a lokacin da aka karanta masa tuhumar a gaban kotu, Emefiele ya musanta aikata laifukan.
Lauyan mai kara, Rotimi Oyedepo (SAN), ya bukaci kotu da ta ware wata rana domin fara shari’a, inda ya ce hukumar na da shaidu da za su tabbatar da aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.
Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa (SAN), ya nemi a bai wa wanda ya ke karewa beli, lamarin da lauyan EFCC bai ki amincewa da shi ba.
A hukuncinsa, Mai Shari’a Yusuf Halilu ya bayar da beli ga Emefiele a kan kudi Naira biliyan biyu da kuma mutane biyu da za su tsaya masa, wanda dole ne su kasance mazauna Abuja kuma su mallaki filaye a yankin Maitama, Asokoro ko Wuse 2.
Alkali Halilu ya ce dole ne Emefiele ya cika sharuddan belin daga ranar Litinin zuwa Laraba, in har bai cika su ba, to za a tura shi gidan gyaran hali.
An dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Yuli, 2025.
