News
Emefiele, karkashin Mulkin Buhari, ya karkatar da kasafin kudin Najeriya na shekaru 10 -Kazaure
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon dan majalisar wakilai, Nuhu Gudaji Kazaure, ya yi ikirarin cewa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya karkatar da sama da Naira tiriliyan 89, kwatankwacin shekara 10 na kasafin kudin Najeriya, a lokacin da yake rike da mukamin Gwamnan Babban Bankin CBN daga 2014 zuwa 2022.
Gudaji Kazaure ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga shahararriyar tashar Hausa ta DCL da Jaridar INDA RANKA ta sa ido a kai.
Yanzu-Yanzu: An Saki Emefiele daga gidan Yari bayan ya cika sharadan Beli
A lokacin gwamnatin shugaba Buhari, Gudaji Kazaure ya jagoranci kwamitin binciken kudaden da Emefiele ya karkatar da su. A yanzu ya yi ikirarin tabbatar da gaskiya ne bisa tonon silili daga kwamitin da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kafa domin binciken zaman Emefiele a matsayin Gwamnan CBN.
Kwamitin da Tinubu ya nada ya bayyana cewa Emefiele ya gudanar da asusu na kasashen waje sama da 593 inda aka boye kudaden Najeriya.
Gudaji Kazaure ya shaida wa Hausa DCL cewa lokaci ya kure masa, inda ya ce a lokacin gwamnatin Buhari ya yi kokarin ganin tsohon shugaban kasar ya ba su damar ci gaba da binciken domin a rubuta sunan tsohon shugaban da rubutun zinariya. Sai dai kash kokarinsu ya kasance a banza.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
