News
Yanzu-Yanzu: An Saki Emefiele daga gidan Yari bayan ya cika sharadan Beli
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya cika sharuddan belin da mai shari’a Hamza Mu’auz na babbar kotun babban birnin tarayya Abuja dake Maitama ya bayar.
Mai shari’a Mu’auz ya bayar da belin Mista Emefiele a kan kudi Naira miliyan 300.
Yanzu-Yanzu: An Saki Emefiele daga gidan Yari bayan ya cika sharadan Beli
An kuma bukaci ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, wadanda tabbas sai sun kasance sun mallaki wata kadara a gundumar Maitama da ke babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Solace Base ta rahoto.
An tattaro cewa sammacin sakin Mista Emefiele yana dauke da sa hannun alkalin hutu, mai shari’a Othman Musa a ranar 22 ga watan Disamba.
Wata majiya a gidan yarin da ta bayyana sakin tsohon gwamnan na CBN ta ce, “An saki Emefiele cikin nutsuwa a gidan yarin Kuje da karfe 3 na yammacin ranar Juma’a bayan ya cika sharuddan belinsa a asirce.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) na ci gaba da nemansa domin ta kama shi,” kuma shi ya sa aka sake shi a asirce.
Ya ce an yi komai a asirce tare da hadin gwiwa da jami’an gidan yarin da suka kammala shirin tare da boye shi daga maziyartan da suka ziyarci gidan yarin.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
