Connect with us

News

Emefiele Ne Ya Mallaki Rukunin Gidaje 753 Da Hukumar EFCC Ta Ƙwace A Abuja 

Published

on

Jami'an Hukumar EFCC Sun Samu Nasarar Karɓe Kadara Mafi Girma Tun Bayan Kafa Hukumar

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Tsohon gwamnan CBN, Emefiele ne ya mallaki rukunin gidaje 753 da Hukumar Yaki da Rashawa da Tattalin Arziki EFCC ta ƙwace a Abuja .

Advertisement

A ranar Litinin hukumar EFCC ta ce ta samu nasarar karɓe gidajen a hannun wani tsohon babban jami’in gwamnati wanda bata fadi sunanshi ba.

Masu Zanga Zanga Sun Yi Wa Majalisar Dokoki Ta Kasa Tsinke Kan Kudirin Gyara Harajin Shugaba Tinubu

Amma wasu takardun shigar da ƙara sun nuna cewa gidan na dakataccen gwamnan babban bankin Nijeriya ne Godwin Emefiele wanda ke fuskantar shari’a.

Advertisement

A cikin takardun kotun da wakilin Jaridar PUNCH ya samu a ranar Talata, EFCC ta bayyana yadda ta gano wannan gida mai girman murabba’in ƙasa 150,500, wanda ke a Plot 109, Cadastral Zone C09, Lokogoma District, Abuja.

Kokarin samun martanin daga lauyoyin Emefiele ya ci tura, domin Matthew Burkaa (SAN) bai amsa kiran waya ko saƙon tes ba a lokacin haɗa wannan rahoto.

Advertisement

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya kare dalilin hukumar na boye sunan mai gidan. Ya ce dokar da aka yi amfani da ita ta ba da damar kwace dukiya ba tare da ambaton sunan wanda ke da ita ba, musamman idan babu wanda ya nuna mallakar abu.

Ya kara da cewa binciken kan al’amarin bai kammala ba, kuma bayyana sunan waɗanda ake zargi ba zai dace ba a wannan matakin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending