Connect with us

News

‘Yan Sanda Sun Gano Masana’antar Kera Bindiga Da Mahaifi Da ‘Ya’yansa Suke Gudanarwa

Published

on

'Yan Sanda Sun Gano Masana'antar Kera Bindiga Da Mahaifi Da 'Ya'yansa Suke Gudanarwa
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar ‘Yan sandan Jihar Akwa Ibom ta rusa wata haramtacciyar masana’antar kera bindiga da wani mahaifi da ‘ya’yansa suke gudanarwa, suna kera bindigogi don sayarwa ga masu aikata laifi a cikin jihar da wajenta.

A yayin taron manema labarai ranar Litinin a Hedikwatar Hukumar dake Ikot Akpan Abia, Uyo, Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar, CP Joseph O. Eribo, ya bayyana cikakkun bayanai kan wannan babbar nasara.

Advertisement

Emefiele Ne Ya Mallaki Rukunin Gidaje 753 Da Hukumar EFCC Ta Ƙwace A Abuja 

An gano wannan haramtacciyar masana’antar kera bindiga ne ta hanyar samun sahihin bayanan sirri daga hukumar, wanda ya sa aka dauki matakin gaggawa daga jami’an ‘yan sanda.

A lokacin da aka kai samame a wurin, jami’an sun kama wanda ake zargi daya, David Nse Emmanuel, yayin da mahaifinsa, Akpan Nse Emmanuel, da ‘yan uwansa, wadanda su ma suna cikin harkar, suka tsere.

A yayin wannan samame, ‘yan sanda sun kwace wasu makamai da suka hada da: sabbin bindigogi guda bakwai na nau’in single-barrel, bindigogi guda biyar na nau’in double-barrel, bindiga guda daya ta musamman mai feda biyu, wata bindigar single-barrel mai rauni, adda mai kama da sanda mai kunnawa, da kuma karafan bututun da ake amfani da su wajen kera bututun bindiga.

Advertisement

 

 

CRIME CHANNEL 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *