Connect with us

News

‎NUJ Ta Karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf A Bikin Cika Shekaru 70 ‎

Published

on

Ƙungiyar Ƴan Jaridu ta  kasa (NUJ) ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo ta musamman bisa goyon bayan da yake bai wa aikin jaridu.

‎An bayar da lambar karramawar ne a wani biki da NUJ ta shirya domin cika shekaru 70 da kafuwarta a birnin Abuja, inda mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya karɓa a madadin gwamnan.

Advertisement

Amurka Ta Sanar Da Kai Hari Cibiyoyi Uku Na Nukiliyar Iran

‎Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Muhammad Idris, ne ya miƙa lambar girmamawar.

‎Shugaban NUJ na ƙasa, Kwamared Alhassan Yahaya, ya ce an zaɓi Gwamna Abba ne saboda irin goyon bayan da yake bai wa kafafen yaɗa labarai da kuma jajircewarsa wajen cigaban ƙasa, kare ’yancin fadar albarkacin baki da inganta shugabanci na gari.

Advertisement

‎A nasa jawabin, mataimakin gwamnan ya taya Gwamna Abba murna, yana mai cewa karramawar ta nuna yadda gwamnatin Kano ke mutunta aikin jarida da ma dimokuraɗiyya baki ɗaya.

‎Kwamared Gwarzo ya kuma bayyana cewa Jihar Kano za ta karɓi bakuncin taron Kungiyar NUJ na gaba.

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending