Connect with us

News

‎Bincike: Al’ummar Tassa Na Fuskantar  Barazana Saboda Hakar Yashi Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano

Published

on

IMG 20250621 WA0015

Wasu mazauna ƙauyen Tassa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a jihar Kano na fuskantar barazana a  rayuwarsu da kuma muhallinsu, sakamakon hakar yashi ba bisa ka’ida ba da ake ci gaba da yi a yankin.

‎Binciken da aka gudanar ya nuna cewa yawan hakar yashin da ake yi ya haddasa Ruftawar kasa ,Rashin Ruwa a rijiyoyi, da kuma lalacewar ƙasar noma a yankin — lamarin da ke barazana ga amfanin gona da rayuwar al’umma.

Advertisement

‎NUJ Ta Karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf A Bikin Cika Shekaru 70 ‎

‎Abdulwahab Dantsoho, wani matashi mazaunin ƙauyen, ya ce tun 2007 suke kai koke-koke, amma ba a ɗauki mataki ba.

‎ “Mun rasa bishiyoyi, ƙasa ta lalace, ruwa ya gurɓace. Gidaje na rushewa, amma babu wani matakin da gwamnati ta dauka” in ji shi.

Advertisement

‎Yahaya Hussaini ya ce rijiyar da ke gaban gidansa ta Rufta, kuma yana cikin fargaba cewa gidansa zai rushe a kansa.

‎ “Ina tunanin barin gida gaba ɗaya saboda tsoro,” a cewarsa.

Advertisement

‎Talatu Abdulrahman, wata tsohuwar manomiya, ta ce ta rasa gonakin mangwaro har kadada uku saboda rashin ruwa da rushewar ƙasa.

‎Muhammad Khamis Garba, wani manomi, ya ce bishiyoyin mangwaro a gonarsa sun mutu gaba ɗaya, inda ya sare su domin amfani da su a matsayin itacen girki.

Advertisement

‎Duk da irin wadannan koke-koke, gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin jawo masu saka jari daga waje domin habaka harkar  ma’adinai a jihar, ta hannun Ma’aikatar Ma’adinai da Albarkatun Ƙasa.

‎Sai dai mazauna ƙauyen na kallon wannan mataki a matsayin rashin damuwa da illar da hakar ke haddasawa ga rayuwarsu da lafiyarsu.

Advertisement

‎ “Al’umma sun gaji da jiran taimako. Idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, to mu da kanmu za mu dauki mataki,” in ji Dantsoho.

‎A watan Mayun 2025, gwamnatin jihar ta fitar da gargadi ga masu hakar yashi ba tare da lasisi ba, tana umartar dakatar da hakan. Sai dai rahoton baya-bayan nan ya nuna cewa umarnin bai sauya komai ba a aikace.

Advertisement

Advertisement

‎STALLION TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending