News
Amurka Ta Sanar Da Kai Hari Cibiyoyi Uku Na Nukiliyar Iran
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanar a daren Asabar cewa sojojin ƙasar sun kai hari kai tsaye kan wasu muhimman cibiyoyin kera makaman nukiliya na Iran.
A cewarsa, jiragen yaƙin Amurka sun kai farmaki kan cibiyoyi uku: Fordow, Natanz da Esfahan — inda suka jefa manyan bama-bamai, ciki har da na musamman masu karfin tarwatsa wuraren da ke karkashin ƙasa.
Mutum Biyu Sun Rasu Yayin Da Suke Ƙoƙarin Ciro Waya Daga Ramin Bandaki A Kano
Trump ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, inda ya ce:
“Mun kammala harin da ya yi nasara sosai a kan wuraren kera makaman nukiliya na Iran. Dukkan jiragenmu sun fita daga sararin samaniyar Iran kuma suna kan hanyarsu ta dawowa gida.”
Harin da Amurka ta kai na zuwa ne bayan fiye da mako guda da Isra’ila ke ta kai hare-hare kan Iran, inda take ƙoƙarin lalata makaman kare kai da kuma ingantattun cibiyoyin nukiliya na Iran.
Rahotannin sun bayyana cewa Amurka ce kaɗai ke da jiragen yaƙi masu ɓoyewa da kuma bama-baman da suka fi karfi – wadanda za su iya lalata cibiyoyin da ke zurfi a karkashin ƙasa.
Sai dai har yanzu hukumomin Iran ba su tabbatar da kai wannan hari ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.
Wannan farmaki yana iya haifar da ƙarin tabarbarewar al’amura a Gabas ta Tsakiya, inda ake fargabar cewa Iran za ta iya kai farmaki kan sansanonin Amurka da ke yankin, ko kuma ƙara harin bama-bamai a kan ƙasar Isra’ila.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
