Connect with us

News

Mutum Biyu Sun Rasu Yayin Da Suke Ƙoƙarin Ciro Waya Daga Ramin Bandaki A Kano

Published

on

waya

Wasu maza biyu sun rasa rayukansu a safiyar Asabar a ƙaramar hukumar Albasu da ke jihar Kano, yayin da suke yunkurin ciro wata wayar salula da ta faɗa cikin ramin bandaki.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne lokacin da Usman Gurgu, mai shekaru 40, ya shiga ramin bandaki domin ciro wayar da ta faɗa ciki, amma sai ya suma a ciki, bai kuma iya fitowa ba.

Advertisement

EFCC Ta Cafke Hadimin Gwamna Kan Zargin Lalata da Kuma  Barazana Ta Intanet

Bayan hakan ne Ibrahim Ƙuyyo, mai shekaru 35, ya shiga domin ceton Usman, amma shima ya faɗi cikin ramin, ya suma, daga bisani kuma ya rasu.

Wani mazaunin yankin mai suna Usaini Mukhtar ya ce rashin ofishin hukumar kashe gobara a yankin ya jinkirta zuwan agaji.

Advertisement

“Na kasance a wajen da abin ya faru. Usman ne ya fara shiga, amma ya jima bai fito ba. Daga nan ne Ƙuyyo ya shiga domin ceto shi, amma shima abin ya shafe shi,” in ji Usaini.

An bayyana cewa daga bisani an ciro gawarwakin mutanen biyu, kuma an binne su bisa tsarin Musulunci.

Advertisement

Kawo lokacin da ake hada wannan rahoton, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin.

 

Advertisement

 

KANO TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending