News
EFCC Ta Cafke Hadimin Gwamna Kan Zargin Lalata da Kuma Barazana Ta Intanet
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta kama mai ba Gwamnan Jihar Benue shawara kan harkokin Rubuce-Rubuce, Bincike da Tsare-Tsare, Dr. Mkor Aondona, bisa zargin cin zarafi ta hanyar lalata da kuma amfani da kafafen sadarwa wajen barazana.
A wata sanarwa da ofishin EFCC na shiyyar Makurdi ya fitar a ranar Asabar, hukumar ta ce an cafke Dr. Aondona ne ranar Juma’a a garin Makurdi, bayan wasu dalibai mata sun shigar da ƙorafi kan yadda yake amfani da matsayinsa wajen tilasta su da su yi hulɗar jima’i da shi.
Wadanda suka shigar da ƙorafin sun zargi Dr. Aondona da neman ‘yan mata ƙanana da sirara da masu kyawun sura domin ba su aiki, amma yana ɗaura sharadin jima’i kafin su samu aikin.
Sun kuma bayyana cewa bayan sun amince da bukatunsa, sai ya riƙa ɗaukar bidiyon saduwar ba tare da saninsu ba, yana amfani da bidiyon a matsayin makamin barazana domin ci gaba da cin zarafinsu.
EFCC ta ce an gano cewa wasu daga cikin bidiyon da ake zargin ya dauka ba tare da izini ba na yawo a kafafen sada zumunta da kuma cikin manhajojin aika saƙo.
A cewar hukumar, “ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma ana shirin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.”
Wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce a jihar Benue da ma kasa baki ɗaya, inda ake bukatar hukumomi su dauki tsauraran matakai kan cin zarafin mata, musamman daga wadanda ke rike da madafun iko.
