Connect with us

News

An Dakatar Da Jami’an Gidan Yari Biyu Kan Zargin Ƙoƙarin Samawa Fursuna Fasfo

Published

on

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) ta dakatar da wasu jami’anta guda biyu bisa zargin ƙoƙarin samawa wani fursuna fasfo, wanda hakan ya saɓa wa ƙa’idojin aiki da kuma dokokin tsaron ƙasa.

Mai magana da yawun hukumar, Umar Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce jami’an da abin ya shafa sun haɗa da wani mataimakin kwanturola da wani abokinsa na aiki.

Advertisement

Bam Yayi Ajalin Mutum 5, Yayin Da Aka Garzaya Da Wasu 15 Asibiti A Kano.

Abubakar ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa wannan aiki na neman fasfo ga fursuna ya sabawa dokokin NCoS da kuma na Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS).

“An gano lamarin ne yayin wani aiki na haɗin gwiwa da ake yi tsakanin hukumomi da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida,” in ji shi.

Advertisement

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne kusan makonni biyu da suka gabata, kuma ya ci karo da ƙa’idojin da hukumar ke bi wajen gudanar da ayyukanta.

Hukumar ta bayyana cewa an dakatar da jami’an da abin ya shafa yayin da ake ci gaba da gudanar da cikakken bincike, tare da shan alwashin ɗaukar mataki mai tsauri idan aka tabbatar da laifin.

Advertisement

Abubakar ya ce hukumar na ɗaukar ladabtarwa da ƙa’ida da muhimmanci matuƙa, tare da jaddada cewa ba za ta lamunci cin hanci, rashin da’a ko wani nau’in zagon ƙasa daga ma’aikatanta ba.

“Mun himmatu wajen tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin gidajen gyaran hali. Duk wanda aka samu da laifi, to hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin da ya dace,” in ji shi.

Advertisement

Hukumar ta kuma bukaci jami’anta da su ci gaba da bin doka da oda wajen gudanar da ayyukansu domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a tsakanin al’umma.

 

Advertisement

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending