News
An Ƙara Kuɗin Yin Fasfo A Najeriya
Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta sanar da cewa daga ranar 1 ga watan Satumba, 2025, za a ƙara kuɗin yin fasfo na ƙasar.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, ACI AS Akinlabi, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce ƙarin zai shafi masu neman fasfo a Najeriya ne kawai.
Cutar Amai Da Gudawa Ta Kashe Mutane Takwas A Zamfara, Fiye Da 200 Sun Kamu
Sanarwar ta bayyana cewa fasfo mai shafi 32 zai koma N100,000, yayin da na shafi 64, wanda zai yi shekara goma kafin ƙarewa, zai koma N200,000.
Sai dai kuɗin da ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ke biya bai canza ba – ana ci gaba da cajin Dala 150 ga fasfo mai shafi 32 da Dala 230 ga na shafi 64.
Hukumar ta ce wannan ƙarin kuɗin na cikin shirin da aka ɗauka don ƙara inganci da tsaron fasfo, tare da tabbatar da cewa ya ci gaba da samuwa ga ’yan ƙasa.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
