News
Ana Shirin Fara Kai Fasfo Har Gida A Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin tarayya ta ce ‘yan Najeriya zasu fara samun fasfo din su har gida ko ofisoshinsu da sauran wuraren da suke so daga shekara mai zuwa.
Ministan harkokin cikin gida O Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Legas yayin da yake jawabi a wajen bikin bude makon jami’ar Legas na 2023.
A cewarsa, nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara morewa tsarin neman fasfo yayin da ma’aikatar ta fara tsara gudanar da aikin.
Ya ce da wannan mataki ‘yan Najeriya ba za su bukaci su jira sama da makonni biyu kafin su samu fasfo ba.
A wani labarin kuma Rundunar sojin Nijeriya ta kaddamar da shirin kwace haramtattun makamai a Filato, Bauchi da kuma Kaduna
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
