Connect with us

News

Wasu Batagari Sun Yi Yunkurin Kubutar Da Masu Laifi A Ofishin Yan Sanda A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Rundunar yan sandan jahar Kano ta samu nasarar cafke wani matashi mai Shu’aibu Sani , dan shekaru 22 mazaunin unguwar Yar’aduwa Kwatas , da aka samu da tabar Wiwi inda jami’an yan sandan suka tafi dashi domin fadada bincike.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa yabaiyana hakan a shafin sa na Facebook

Advertisement

Ana Shirin Fara Kai Fasfo Har Gida A Najeriya

SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa a lokacin da jami’an su, na Zango suna aiki a ranar 9 ga watan Oktoba 2023, suka samu nasarar cafke matashin dauke da tabar Wiwi a jikinsa, wadanda suka tafi dashi ofishinsu dan fadada bincike kan lamarin.

 

Advertisement

Sai dai wasu batagarin matasa dauke da makamai da Duwatsu, wadanda suka yi cincirindo a ofishin yan sandan suna yin jifa, tare da yunkurin kubutar da matashin da aka cafke da sauran wadanda suke tsare a ofishin yan sandan.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa matasan sun farwa jami’an yan sandan , inda daya daga cikin su ya harbi kanin wanda aka kama mai suna Inuwa Sani, agefan hannunsa, daganin hakanne sauran matasan suka tarwatse.

Advertisement

Jami’an yan sandan sun dauke shi tare da kai shi Asibiti aka duba lafiyar sa tare da dankashi a hannu mahaifinsa dan ci gaba da kula da lafiyarsa.

Wanda ake zargi da mallakar tabar Wiwin ya tabbatar wa da jami’an yan sanda cewa, kanin nasa yana da lalurar kwakwalwa, domin koda a shekarun baya sai da ya taba cire masa dan yatsa da wuka, a lokacin da ya yi yunkurin cakawa mahaifiyarsu wukar shi kuma ya rungume shi.

Advertisement

 

Ya kara da cewa sun taba kai shi Asibitin kula da masu lalurar kwakwalwa dake Dawanau Kano, kuma ya samu ya sauki , amma lokaci zuwa lokaci abun yana motsa masa.

Advertisement

SP Abdullahi Haruuna Kiyawa, yaja hankalin al’umma da cewa aikin su shi ne kare rayukan al’umma da dukiyoyin su .

 

Advertisement

A karshe ya ce duk wanda ya fito, dan tayar da hankulan jama’a ko masu ta’ammali da kayan maye da yan fashi da makami da masu kwace ko fadan daba , ba za su saurara musu ba domin zasu cafke su , a gudanar da bincike sannan a gurfanar dasu a gaban kotu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending