News
Rundunar yan sanda ta kama wanda Ake Zargi Da Laifin Kisan kai a Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar yan sandan jahar Kano ta cafke wani matashi mai suna Abdullahi Sagir ( Yellow) mazaunin unguwar Dan-Agundi dan shekaru 25, da wasu abokansa Nababa da kuma Umara da ake zargi da aikata laifin kisan kai.
Tunda a ranar 4 ga watan Oktoba 2023, ake zargin matasan sun farwa wani matukin Adaidaita Sahu mai suna Muhammad Jamilu Kofar Nasarawa, da makamai wadanda suka sassareshi wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abudullahi Haruna Kiyawa, ya baiyana haka a cikin wata Sanarwar da ya fitar a shafin sa na Facebook
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Binciken yan sandan na farko-farko ya kai ga kama daya daga cikin matasan da ake zargi mai suna Abdullahi Sagir ( Yellow) , inda ya tabbatarwa da yan sanda cewa sun farwa mutanen Kofar Nasarawa dauke da makamai.
” mu yan unguwar Dan-Aguundi mun fito fadan daba akan mutanen unguwar Kofar Nasarawa, inda Abokina Nababa ya fara buga masa wuka , shi kuma Umara ya sareshi aka, ni kuma na kafta masa Adda a bayansa.
” Na yi nadamar aikata laifin kisan kai da na aikata , amma ban shirya mutuwa, a cewar matashin da ake zargin.
A karshe mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce kwamishinan yan sandan CP Muhammad Usaini Gumel , ya bada umarnin dawo da batun babban sashin gudanar da binciken manyan laifukan kisan kai dake Bompai , dan fadada bincike akansa kuma da zarar an kammala za a gurfanar da shi a gaban kotu dan ya fuskanci hukunci.
A wani labarin kuma Yadda Bankuna Suka Koka Kan Samun Karancin Takardun Kudi A Jihar Kano
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
