News
Rundunar sojin Nijeriya ta kaddamar da shirin kwace haramtattun makamai a Filato, Bauchi da kuma Kaduna
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar Sojojin Nijeriya ta kaddamar da wani gagarumin shiri na kwace haramtattun makamai daga wurin bara-gurbi a jihohin Filato da Bauchi da kuma Kaduna.
Kwamandan rundunar Operation Safe Haven Janar AE Abubakar, wanda ya kaddamar da shirin a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato a ranar Talata, ya kara da cewa babban burinsu shi ne a samu cikakken tsaro a jihohin da ma fadin Nijeriya.
Gwamnonin Arewa maso Yamma sun tsara hanyoyin da za a bi don ci gaban tattalin arzikin yankin
Jihar Filato ta kwashe shekaru aru-aru tana fama da rikicin kabilanci musamman tsakanin ‘yan kabilar Birom da kuma Fulani, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane. Su ma jihohin Kaduna da Bauchi na fama da irin wadanda matsaloli, ko da yake a yanzu hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun fi damun jihar Kaduna.
Janar Abubakar ya ce “dole ne hukumomi su magance silar rikice-rikicen da ke addabar” jihohin “domin a kawar da rashin tsaron da ke damun al’ummominsu”.
“A yayin da nake mika umarnin Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya cewa dole ne a dauki dukkan matakin da ya kamata na hana bazuwar rikici a karamar hukumar Mangu, ina kira a mutunta sarakunan gargajiya a matsayinsu na masu wanzar da zaman lafiya,” in ji Janar Abubakar.
A nasu bangaren, sarakunan gargajiya sun sha alwashin ci gaba da goyon bayan hukumomin tsaron Nijeriya a yunkurinsu na wanzar da zaman lafiya a kasar.
A wani labarin kuma Gwamnonin Arewa maso Yamma sun tsara hanyoyin da za a bi don ci gaban tattalin arzikin yankin
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
