News
Cutar Amai Da Gudawa Ta Kashe Mutane Takwas A Zamfara, Fiye Da 200 Sun Kamu
Annobar cutar amai da gudawa (Cholera) ta sake ɓulla a wasu sassan Jihar Zamfara, inda rahotanni ke nuna cewa akalla mutane fiye da 200 daga ƙauyuka 11 na Ƙaramar Hukumar Bukkuyum suka harbu da cutar.
Mazauna yankin da ma’aikatan lafiya suka shaida wa kafar labarai ta Reuters cewa cutar na ci gaba da ƙara kamari, tare da sanar da mutuwar akalla mutane takwas a yankin, sakamakon ƙarancin magunguna da matsalar tsaro da ta dabaibaye jihar.
Cutar Cholera wacce ake yawan ɗaukowa ta hanyar shan ruwan datti ba sabuwar cuta ba ce a Najeriya, inda a lokuta da dama ake samun bullarta tare da haddasa asarar rayuka. A farkon wannan shekara ma, annobar ta kashe mutane da dama a jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto da Neja, yayin da shekaru biyu da suka gabata aka shaida bullar cutar a kusan faɗin ƙasar, inda ta yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane a jihohin Lagos da Kano.
Masana harkokin lafiya sun danganta sake bullar cutar a Zamfara da matsalar ƙarancin tsaftataccen ruwan sha, matsalar da ta addabi Najeriya baki ɗaya, musamman a yankunan karkara.
Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan yankunan da cutar ta fi kamari sun haɗa da Nasarawa-Burkullu, Gurusu da Dabka, inda mafi yawan masu fama da cutar ke samun kulawa ne a gidajensu saboda tsaro da rashin isassun cibiyoyin lafiya, abin da ke iya ƙara tsananta halin da ake ciki.
Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, hukumomin Jihar Zamfara basu fitar da wata sanarwa kan sake bullar cutar ba.
