News
Ɗalibar Ajin Ƙarshe A Poly Ta Rasu Yayin Zubar Da Juna Biyu
Wata ƴar shekara 26 da ke ajin ƙarshe a makarantar Polytechnic da ke Lokoja a jihar Kogi ta gamu da ajalinta a lokacin da ta yi yunƙurin zubar da cikin wata shida a wani asibitin kuɗi.
A cewar Zagazola Makama, wanda mai sharhi ne akan lamuran tsaro, ya ce al’amarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Agusta, 2025 a Asibitin Alhassan Clinic and Maternity da ke yankin Sarkin Noma a babban birnin jihar.
Marigayiyar mai suna Omotosho Dorcas tana ɗauke ne da juna biyun wata shida inda ta je asibitin da neman a zubar da shi. A yayin haka ta rasa ran nata sakamakon kwarara jini daga jikinta.
Majiyoyi sun ce tuni jami’an ƴan sanda suka garzaya wajen da abin ya faru inda suka ɗauki hotuna da kuma ɗauke gawar zuwa Babban Asibitin Tarayya da ke Lokoja.
Haka kuma sun shaida cewa, an kama wanda ya jagoranci al’amarin yayin da aka miƙa shi ga cibiyar bincike manyan laifuka ta jihar (SCID) domin cigaba da gudanar da bincike akansa.
Wannan ba shi ne karo na farko da irin haka yake faruwa ba, domin kuwa a shekarar 2020, wata ɗaliba a Jami’ar Ambrose Alli da ke Jihar Edo mai suna Gift Imoluamen ta rasu a lokacin da ta yi yunƙurin zubar da juna biyu bayan zargin wani fasto a wani sanannen coci a jami’ar da alhaki a kai.
Imoluamen ta kasance ƴar aji uku ce a tsangayar nazarin siyasa a lokacin da abin ya faru.
