Connect with us

News

Yansanda Sun Cafke Matasa 51 Da Ake Zargi Da Fadan Daba A Kano 

Published

on

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce ta cafke matasa 51 da ake zargi da hannu a cikin ayyukan daba a sassa daban-daban na birnin, cikin kwanaki uku da suka gabata.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce wadanda ake zargin an kama su ne da makamai da kuma kayan maye.

Advertisement

NUJ Za Ta Karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf Da Lambar Girmamawa

“Ina so in sanar da al’umma cewa cikin kwanaki uku kacal mun kama matasa 51 da ake zargi da aikata ayyukan daba a wasu yankuna na jihar,” in ji SP Kiyawa.

Ya ce bincike na farko ya nuna cewa matasan suna da alaka da hare-hare da tayar da tarzoma a unguwanni da dama, tare da cin karen su babu babbaka.

Advertisement

Kiyawa ya kara da cewa rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike, kuma za a fitar da cikakken bayani game da sunayen wadanda aka kama da kuma makaman da aka samu a hannunsu.

A ‘yan makonnin nan, mazauna wasu unguwanni a Kano kamar su Kurna, Dakata, Fagge, Dala da Hotoro na yawan korafi kan yadda ‘yan daba ke tada rikici da tsoratar da jama’a da zarar rana ta fadi, lamarin da ke zama barazana ga zaman lafiya da harkokin yau da kullum.

Advertisement

Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri da farautar bata-gari domin tabbatar da tsaro a jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending