Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Bankado Ma’aikatan Bogi 247, Ta Karɓo Sama Da Naira Miliyan 27

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta gano wasu kura-kurai masu girma a tsarin biyan albashi, ciki har da ma’aikata 240 da ke karɓar albashi sau biyu.

Dakta Sulaiman Wali Sani, mashawarcin musamman ga gwamna kan harkokin ma’aikata kuma shugaban kwamitin gudanarwa na tsaftace tsarin albashi, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai a Kano.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Bankado Ma’aikatan Bogi 247, Ta Karɓo Sama Da Naira Miliyan 27

Dakta Sani, wanda ya wakilci Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) a taron, ya ce wannan bincike na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin gyara da inganta tsarin biyan albashi a jihar.

Ya bayyana cewa binciken ya samo asali ne daga wani aikin tantance ma’aikata da kuma aikin kwamitoci guda biyu da aka kafa, musamman domin duba yadda ake biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomi.

Advertisement

Baya ga ma’aikatan da ke karbar albashi sau biyu, Dakta Sani ya kara da cewa ma’aikata 1,335 sun kasa gabatar da bayanan da ake bukata domin tantance su har fiye da watanni shida, lamarin da ke kara jefa shakku kan sahihancin sunayensu a cikin tsarin biyan albashi na gwamnati.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da aikin tsaftace tsarin domin tabbatar da cewa kudi na gwamnati ba su ci gaba da zubewa a hannun wadanda ba su cancanta ba.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending